Korona: ‘Hukumar NCDC ta ci mutuncin Hausawa da yaren Hausa’

dakikun karantawa

An bayyana wata sanarwa da hukumar kula da cututtuka ta Najeriya ‘NCDC’ ta fitar a matsayiin cin mutunci ga yaren Hausa da kuma rashin mutunta Hausawa.

DABO FM ta tattara cewar a ranar Lahadi, hukumar NCDC ta fitar da wata sanarwa ta jan hankalin mutane kan cigaba da kare kawunansu ga abubuwan da suke kara saka cutar Korona ta yadu a tsakanin mutane.

Hukumar ta wallafa hotuna guda 4 masu dauke da sakonnin yadda za a kare yaduwar cutar Korona, ta wallafa hotunan da yare 4 da suka hada da Hausa, Inyamuranci, Yarabanci da kuma Turanci.

Sai dai rubutun Hausar da NCDC ta saka a sakon bai nuna alamun Hausa ake ba, hasalima masana sun bayyana rubutun Hausar a matsayin ‘shirme, sakarci ko kuma maganar banza.’

Hukumar ta rubuta; “Kaunna Tanna Kiyayewa – Guju runguma da shanyannu tare da kaunatattun mutane don hana yaduwar cutar Covid-19, hukumar ta rubuta ne a maimakon “Ku guji gaisawa da rungumar masoyanku domin kauce wa yaduwar cutar Covid-19.”

Wani malami a Jami’ar Bayero da ke Kano, Muhammad Sulaiman Abdullahi ya bayyana rubutun Hausar da hukumar ta saka a matsayin cin mutunci tare da furta kakkausar kalma da cewa ‘tsabagen rashin mutunci.’

“Wannan cin mutunci ne!”

Malamin ya ce ya tuntubi hukumar domin bada gudunmawa kan ayyukan wayar da kai cikin harshen Hausa wanda a cewarsa duniya ta karba kuma tana amfani da su.

Sai dai ya ce basu yi masa martani ko guda daya ba kan tarin sakonnin da ya aike wa hukumar ba.

Kalli sanarwar daga NCDC

Karin Labarai

Sabbi daga Blog