Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Ana ta kama masu wakokin nanaye an bar masu barna da sunan addini suna zagin Allah – Sheikh Daurawa

2 min read

Tsohon shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, yayi kira tare da yin suka akan Hukumar tace fina-finai da wakoki ta jihar Kano.

Ya bayyana cewa ana kama ‘yan fim, a kyale masu yiwa Allah Izgili.

Kira irin na hikima, Daurawa ya shawarci hukumar da ta fadada aikinta wajen farautar wadanda suke yiwa Allah Izgili da fadar kalmomin da basu dace ba da sunan wakokin yabo.

DABO FM ta binciko tare da tabbatar da cewa; Kalaman malamin, basu da alakar kusa ko ta nesa da aikin da Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano take yi na kama mawaka da yan fim a yanzu.

Tuhume-tuhumen da ake alakantawa da Siyasa.

Sheikh Daurawa, yayi kalaman ne dai dai lokacin da yake amsa tambayar wani dalibi akan “Bambancin Waka da Wake.”

Bayan dogon bayani, malamin yazo kan gabar wakokin yabo, inda ya bada kissa akan wasu mawaka da ma’aikin Allah (SAW) ya dakatar da yin wakensu a lokacin da suka ce ambaci shi (Manzon Tsira (SAW)) a matsayin wanda yasan abinda zai faru gobe.

Wakilin DABO FM da ya halarci karatun da aka gudanar a masallacin Ansarussunnah dake Fagge ya rawaito malamin yana cewa;

“Akwai hukumar tace fina-finai ai, tana kama wadanda suka saba ka’ida. To su wakokin annabi babu mai tace su?”

“Babu hukumar da zata tace yabon Annabi, ta tace irin kalmomin da ake gayawa Allah, ta kama masu wakoki da musu ladabi tayi musu bita ta koya musu yacce ake yabon.”

“Ana ta kama masu wakokin nanaye, ga masu barna da sunan addini, ga masu zagin Allah, ga wadanda suke fadawa Annabi (SAW) kalmomin da babu ladabi.”

“Su yakamata a nusantar a gaya musu ga yacce akeyi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.