Labarai

Annabi Muhammad, ma’aunin zaman lafiya da jinkai – Rochas Okrocha

Tsohon gwanan jihar Imo kuma Sanata mai wakiltar Imo ta yamma, Rochas Okrocha, ya bayyana Annabi Muhammad SAW a matsayin bangon ma’aunin zaman lafiya da hadin kai.

Rochas yayi kira ga al’ummar Musulmi da su rika yin koyi da Shugaba SAW wajen tafiyar da rayuwarsu domin tabbatar da zaman lafiya da jin kai.

“Akwai muhimman darussan da za’a koya daga rayuwa da koyarwar Annabi Muhammadu SAW. Ya kasance ginshikin aminci da haɗin kai.”

Rochas Okrocha ya bayyana haka ne ta hannun mataimakinshi a fannin labarai, Ahmad Mustapha, a ranar Litinin, kamar yacce kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya rawaito.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ba mu ba APC – Rochas

Dabo Online
UA-131299779-2