Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana ware Naira biliyan 1 domin ginin Masallatan Juma’a, gyaran Makabartu, Ciyarwar Azumi da wasu ayyuka na sha’anin addini Islama a shekarar 2020.
Kwamishinan Ma’aikatar sha’anin addinai, Sheikh Tukur Jangebe ne ya bayyana haka yayin da yake kare kasafin kudin da ma’aikatar tayi a gaban Majalissar jihar dake garin garin Gusau a jiya Laraba.
DABO FM ta tattaro cewa Sheikh Jangebe yace za’a kashe sama da Naira miliyan 300 domin ciyarwa da taimako a yankunan karkara a lokacin azumin watan Ramadana.
“Kun sani cewa a duk lokacin Ramadan, a karkashin wanna ma’aikata, gwamnatin jiha tana bude cibiyoyin ciyarwar a fadin jiha baki daya.”
“A wannan lokacin, muna son fitar da sabon tsarin ciyarwa a fadin jihar, muna so muyi tsarin domin mutanen karkara sun amfana sosai a cikin wannan shirin.”
DABO FM ta tattara cewa ya sake bayyana cewa a karkashin kasafin kudi na shekarar 2020 da ya gabatar, ma’aikatar ta tsara gina karin Masallatan Juma’a guda 17 a yankin kowacce Masarauta dake jihar.
Ya kara da cewa za’a gina manyan Makarantun addinin Musulunci a kowanne yanki 3 dake jihar.
“Mun fuskanci yawanci daga cikin makabartun jihar sun rusa tare da cewar wasu guraren ma basu da ita gaba daya.”
“Zamu gyara dukkanin makabartun da suke a kananan hukumominmu 14 tare da samar da wasu sabbi a guraren da ake da bukata.”
Ya kara da cewa shirin ma’aikatar ya kunshi kara albashi na Malaman masallatan Juma’a na jihar, ya tabbatar da ware kudin wa’azi/da’awa duk a cikin kasafin kudin na shekarar 2020.
