Attajiran ne suke da hakkin samawa Matasa aiyukan yi – Sarki Sunusi

Mai martaba Sarkin Kano, Mallam Muhammad Sunusi na biyu yace attajiran jihar Kano ne suke da hakkin samawar da matasa aiyukan yi a fadin jihar Kano.

Sarkin ya ce Alhaji Aliko Dangote da Abdussamadu Isyaka Rabi’u sune ke da hakkin samarwa da matasa aikin yi a jihar Kano.

Sarkin ya bayyana haka ne a wajen wani taron kungiyar “Kano Concerned Citizens Initiative” wanda aka gudanar a dakin taro na jami’ar Bayero dake Kano.

Yayi kira ga Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Abdussamdu Isyaka Rabi’u da suyi kokari wajen gina jihar Kano ta yacce zasu tallafawa al’umma musamman matasa domin kubutar dasu daga cikin halin kunci da talaucin da ake ciki.

Sarki yace su yi taimako cikin hanzari nan da shekaru 200 masu zuwa alheran da suka yi ba za su gushe ba.

Mai martaba Sarki yayi kira ga Attajiranda su ci gaba da ginin ganuwar Kano wanda wasu turawa suka faro aikin wani bangare ba’a karasa ba, ya ce gwamnati kadai ba zata iya magance matsalolin da suke addabar al’umma ba.

Sarkin ya kara da cewa dole da shi  manyan attajiran ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bada duk wata gudunmawa kama daga zuwa Bankin Duniya zuwa ko ina ne wajen nemo wa jihar Kano tallafin da zai ciyar da garin musamman a banagaren Ilimin Matasa Mata da Maza.

Har ila dai Mai Martaba Sarki yayi magana akan bunkasa sana’o’i da koyar dasu domin amfanar mata musamman wadanda suke zaune a gidajen mazajensu babu abin yi.

Inda ya yi maganar kawo masana’antu na sarrafa takalma da jakunkuna tare da amfani da auduga don sarrafa rigunan zamani wadanda za’a dinga siyarwa a wajen Kano dama kasa baki daya.

A karshe sarki ya yi kira ga shugabannin siyasa da su taimaka su hadu waje daya su samarwa mata gurabe a cikin harkokin mulki, yace a bawa mata damammakin da su ka dace don su yi magana da muryar ragowar matan da suke cikin gida.

Sarki yace daga rana irin ta jiya dukkanin matsalolin da aka tattauna zasu zama tarihi a jihar Kano da yardar Allah.

%d bloggers like this: