Nishadi

‘Yan Matan Arewa sun fara tallar kansu ga Mazan Aure tin bayan Auren yaro ‘dan shekara 17

Tin bayyanar auren Abba, yaronnan mai shekaru 17, mata dayawa a shafukan sada zumunta suka bullo da wata sabuwar hanyar neman mazan aure musamman a manhajar Instagram.

Bayan bincike da wakilinmu Muhammad Aliyu ya gudanar a manhajar Instagram, ya binciko wani shafi mai suna “Northern Blog”, shafi ne dake tattauna batutuwan Matasa da matsaloli na ma’aurata tare da neman shawara ko bukatar a duk sanda hakan ta taso.

Tin bayan fitowar magana akan auren wasu yara matasa guda 2, ‘yan mata suke ta tura bukatarsu zuwa ga shafin Northern Blog neman samun dace ko akwai wanda zai yaba yayi magana domin neman auranta.

Matan sukan rubuto sunan su, garin da suke zaune, shekarunsu da dai wasu abubuwa game da su, haka kuma wasu sukan bayyana irin kalar mijin auren da suke so kamar yadda zaku gani a hoto na kasa.

Wannan hoto na sama, wata budurwa ce ta aiko da sako inda take bada bayanan kanta ga duk saurayin da yaga tayi daidai ga ra’ayinshi.

“Aure nake so wallahi, Ina da Shekara 23, ni wankan tarwatsa ce, O+ ne nau’in jini na, ina da nau’in kwayar halitta ta AA, Ina karanta Nazarin addinin Islama a jami’ar gwamnatin jihar Kaduna. Ina da kiba kadan kuma ni ‘yar jihar Kaduna ce.

Daga NB

Wannan hoto na sama, wata matashiya ce inda ta turo domin a tayata yiwa kannenta cigiyar saurayin da hotonshi ya fito, tayi haka bisa yadda ‘yan uwanata suka nuna damuwarsu akan saurayin.

‘Yan matan na turowa ne da saka tsammani cewa zasu samu mijin aure a yanar gizo-gizo, inda wasu sukanyi alamun yin kuka da roko mai tsanani cewa a taimaka musu wajen nemo musu saurayin da suka aiko da hotonshi.

Daga Shafin NB

Wannan ma wata matashiya ce ‘yar jihar Kano, inda itama ta bukaci a taimaka mata domin neman mijin aure.

“Ni mace ce mai shekaru 23, daga Kano, Ina neman namiji, Bahaushe, mai rikon addini wanda ya shirya yin aure, mazaunin Kano, Kaduna ko Abuja.”

Ko tsoho ne indai shine alheri. A kullum alheri muke nema. Allah yasa mu dace. Ina rokon Allah ya saka muku da alkhairi.”

Ku bibiyemu gobe inda zamu kawo muku yacce suma mazan ke neman matan aure a kafafen sada zumunta.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ina ganin laifin Talakawa, da mutum ya samu kudi sai su yanyameshi – Aisha Falke

Dabo Online

‘Yan Matan Arewa sun bukaci a fara yiwa mazaje gwajin hauka kafin a daure musu aure

Dabo Online

Naman Sallah hakkin Iyayen Samari ne – Martanin ‘Yan mata zuwa ga Samari

Dabo Online

An daura wa yaro dan shekara 15 aure da budurwarshi ‘yar 14 bayan yayi mata ciki

Dabo Online

‘Yan Mata sun fara kokawa kan yadda samari sukayi ƙememe suka hana su kayan Sallah

Dabo Online

Zauren Maza da Matan Arewa a Instagram ya hada dubu dari 850 don tallafawa Jarumi Moda

Dabo Online
UA-131299779-2