Aisha Buhari zata gina katafariyar Jami’ar Kudi mai zaman kanta

Karatun minti 1

Uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Muammadu Buhari ta bayyana shirin ta na gina jami’ar Kudi a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Haj Aisha Buhari ta bayyana haka ne a jiya Asabar yayi wani taro da wasu ‘Yan kishin kasa a jihar Adamawa.

Daily Trust tace, Aisha bata bayyana a ina zatayi makarantar ba, haka kuma bata bayyana yaushe zatayi makarantar ba.

Sai dai tace za’a gina makarantar ne bisa wata hadin gwiwar daga kasar Sudan da Qatar.

Aisha ta bayyana kukanta kan yacce harkokin Ilimi suka tabarbare, inda ta bayyana zata bada tata gudunmawar wajen inganta harkar Ilimi a jihar Adamawa.

“Ina mai bada shawara kan kafa Asusun Aiyukan Cigaba wanda zai tamaka wajen bada gudunmwar samar da abubuwa da jihar tak bukata na cigaba.”

Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito wasu daga cikin mahalarta taron.

Daga cikin masu jawabi akwai Amb Fatima Ballah, Alhaji Sadik Daware, Prof Shehu Iya , Prof Auwal Abubakar and Mrs Helen Mathias.

Taron dai ya samu halartacin wasu daga manyan yan siyasar jihar na jami’iyyun ADC, APC da PDP.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog