Babban Labari Labarai

Azumi na koyar da kauna ne da soyayyar juna-Ibrahim Madalla

A sakon sa na barka da sallah da taya al’ummar musulmi murnar kammala Azumin watan Ramadana lafiya, wani shugaban al’umma a karamar hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Garba Umar Madalla, ya roki Allah kada ya mai-maita wa al’umma halin da aka shiga a sallar bana saboda cutar sarkewar numfashi ta Covid-19.

Ibrahim Garba Umar, ya bayyana haka ne da yake zantawa da Dabo FM a Zariya.

Ya ce, duk da an kammala Azumi lafiya, amma halin kuncin da al’umma musamman wanda ba su da cin yau ballantana na gobe suka shiga, akwai bukatar al’umma su koma ga Allah madaukakin Sarki su naimi yafiyar sa dalilin zunuban da ake aikatawa na yau da kullum. Inda ma ya kara bayyana cewar, azumi na koyar da kauna ne da soyayyar juna.

Ya bukaci shuwagabanni musamman masu jagoranci su ji tsoron Allah akan dukkanin abubuwan da suke aikatawa kasancewar dole a rika lura da rayuwa da dukiyoyin al’umma.

Kuma su tuna rantsuwar da suka yi da Al-qur’ani game da jagoranci al’umma.

Ya roki al’umma su kasance masu yi wa kasa addu’a a koda yaushe kuma su yi amfani da darussan da suka koya lokacin azumin watan Ramadana.

Da ya juyo ga Jihar Kaduna kuwa, Alhaji Ibrahim Madalla, ya kwatanta matakan da gwamnatin ta dauka a matsayin wanda sam basu dace ba, saboda halin da kuncin da al’umma je ciki musamman marasa galihu.

Ya taya Mai Martaba Sarkin Zazzau kuma shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kaduna da al’ummar masarautar Zazzau da Jihar Kaduna da kuma Najeriya baki daya murna, saboda ganin karamar sallar bana.
Sannan ya roki Allah ya mai-maita cikin koshin lafiya da aminci.

Karin Labarai

UA-131299779-2