Labarai

Kwabid19: Ruwan sama ya fara hallaka abincin tallafin da Buhari ya aiko Kano

Ruwan sama ya fara lalata abincin tallafin rage radadi da gwamnatin tarayya ta aikowa jihar Kano, kayan tallafin da ya hada da shinkafa, masara, gero da sauran kayan abinci na fuskantar baraza bayan da aka zube su a tsakar wajen kamfanin manoma na jihar ba tare da killacesu ba.

Majiyar Dabo FM daga Solacebase.com ta bayyana gwamnatin Kano tayi wasarere da kayan tallafin a tsakar filin kamfanin taki na Kasko dake Farm Center ba tare da an adana suba, wanda sau 3 ruwan damina yana sauka akan su.

A halin yanzu buhuna da dama na cikin ruwa tsamo tsamo, baya ga beraye da kwari da suke bikin sallah a kan kayan abincin.

A ta bangaren shigaban kwamitin hada tallafin jihar Kano, Farfesa Yahuza Bello wanda shine shugaban jami’ar Bayero ya bayyana cewa sun shirya tsaf ranar Talata za’a fara raba kayayyakin abincin ga masu karamin karfi a jihar.

Karin Labarai

UA-131299779-2