Home LabaraiBabban LabariKada ku bari halin da ake ciki ya durkusar da bangaren Ilimin Kasar nan – Habiba Muhammad

Kada ku bari halin da ake ciki ya durkusar da bangaren Ilimin Kasar nan – Habiba Muhammad

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

Shugaban wata Cibiya mai kula da Ilimin ‘ya’ya mata a Najeriya, wato Center For Girls Education a turance Hajiya Habiba Muhammad, ta bayyana muhinmancin ranar da aka ware domin tunawa da yara kananan a matsayin mai muhinmancin da zai sa yaran cikin farin ciki tare da nazari a kan rayuwar su da sanin ina aka dosa a duk shekara idan an zo tunawa da irin wannan rana.

Tana bayyana haka ne da take zantawa da manema labarai ciki har da Dabo FM, da kuma ta ke tsokaci game da ranar tunawa da kananan yara ta bana.

Dama dai majalisar dinkin duniya ne ta ware duk ranar 27 ga watan mayu domin tunawa da yara kananan a fadin duniya, Kuma duk shekara akan shirya bukuwan ne na wasanni tare da shirya hanyoyin sa su nishadi.

Duk da bukin na bana, na zuwa ne dai-dai lokacin da duniya ke fama da cutar sarkewar numfashi ta Covid-19 da ta addabi duniya ciki kuwa har da nan Najeriya.

Ta ce, kasancewar yaro a matsayin mai lura tare da nazari akan lamuran da ke faruwa a rayuwa, irin wannan rana kan sanya su natsu kuma su gane muhinmancin da ke tattare da tunawa da su kansu da ma muhinmancin su cikin al’umma.

Sai dai ta hori yaran su cigaba da kasancewa masu naiman Ilimi da duk wani abu da zai afane su kuma ya amfani rayuwar su a matsayin su na masu tasowa.

Hajiya Habiba Muhammad, ta kuma yi tsokaci game da Ilimin ‘ya’ya mata wanda a ciki har ta yaba ma gwamnatin Jihar Kaduna bisa manufofin da ta bullo da shi da hakan ya saukakawa mata wurin naiman Ilimin zamani da na addini.

Ta yi fatan sauran jahohi su yi koyi da salon gwamnatin Kaduna wurin baiwa mata ilimi kyauta.

Ta nanata ganin halin da ake ciki bai durkusar da fannin ilimi ba, saboda ma ga sabon tsarin da aka bullo da shi na koyar da yara ta rediyo da sauran sabbin fasahohi.

Ta kara da cewa, yawancin kalubalen da Ilimin ‘ya’ya mata ke fuskanta, shi ne rashin samun cikakken goyon baya daga wurin iyaye, inda sau da yawa akan fifita karatun maza fiye da na mata duk da su ne jigon cigaban kowacce al’umma.

“Mu a Cibiyan mu muna koyar da mata ilimi tare da basu horo akan wasu fannoni da zasu kware da kuma ake sa ran hakan ya kara inganta rayuwar su ko da a gidajen aure ne, kuma muna aiki ne a nan Jihohin Kaduna da Bauchi Sokoto da Kebbi da kuma Gwambe”, inji Habiba Muhammad.

Sai dai ta koka akan yadda ake samun karuwan cin zarafin mata musamman a yankin Arewacin Najeriya, duk da su kan su a cibiyar su sun kware ne fannin koyar da matan hanyoyin kariya kafin ma a samu irin wannan kalubalen.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00