Gaskiya ba ta bukatar ado: Nadaina Zuwa Coci, saboda Addinin Kiristanci akwai alamar tambaya

  • Fitacciyar jarumar kasar Ghana, Efia Odo ta bayyana wani dalilinta da ya sanya ta daina zuwa coci ibada kwata-kwata

Jarida Hausa Legist ta rawaito cewa Jarumar ta ce ita ta kasa gane inda addninin Kiristanci ya sanya gaba, shine yasa ta daina zuwa cocin

  • Ta ce ta yadda cewa akwai Allah kuma ta yadda da Annabi Isa, amma kuma gaskiya addinin Kiristanci ta san cewa akwai rudani a cikin shi

Fitacciyar jarumar kasar Ghana, Efia Odo ta bayyana cewa ta daina zuwa coci ne kwata-kwata bayan ta kasa gane inda alkibilar addinin Kiristanci ta sanya gaba.

Jarumar wacce kuma take wani shiri a gidan talabijin na Kwase TV, ta bayyana cewa ta yadda kwarai da gaske akwai Allah sannan kuma ta yadda da Annabi Isa, amma kuma addinin Kiristanci yana da rudani masu yawan gaske a tattare dashi da suke da rikitarwa.

“Lokacin ina yarinyar karama ina zuwa coci a kowanne lokaci, ina bin mahaifiyata muje tare, amma lokacin dana girma sai na daina zuwa, saboda na kasa gane alkibilar wannan addinin namu,” in ji ta.

Da aka tambayeta akan tsattsauran ra ayi, Efia Odo ta ce a cikin hirar ta su:

“Ni ba mace ba ce mai tsattsauran ra’ayi. Ina yin rayuwata ne yadda naga ta fi mini, ya rage naku ku yadda da abinda na fada ko karku yadda.”

Jarumar dai ta kasar Ghana yanzu ne tauraruwar ta ke haskawa a masana’antar fina-finai ta kasar Ghana.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: