Za a fara yiwa ‘yan Najeriya da sukayi a Digiri a kasashen ketare binciken kwakwaf

Domin kara tsaftace harkokin Ilimi a fadin kasar nan, Gwamnatin tarayya za ta fara tantance takardun Digiri da ‘yan Najeriya sukai a kasashen ketare.

Ministan Ilimi na kasa, Malam Adamu Adamu ya sanar da haka, inda ya tabbatar da cewa, dole ana tantance takardun don samun tabbacin ingancin karatun ‘yan Najeriya a wadannan kasashe.

Ministan ya kara da cewa, wasu Jami’oin suna gudanar da harkokin karatu ne, ba tare da hukumomin ilimi sun tantance su ba. Ya kara da cewa, akwai jami’oin da suke da hakikanin cewa ba a tantance su ba a wasu kasashen Afirka da suka hadar da:
Ghana, Togo, Kwatano, da kuma Kamaru.

Masu Alaƙa  Zamu fara kama iyayen da basa saka 'yayansu a makaranta - Malam Adamu

Ministan ya bayyana haka ne, a wurin taron tabbatar da tsayayyen Ilimi na kasa karo na 33, wanda ya gudana a Abuja.

Ministan ya kaddamar da kwamati a kan wannan aiki da ya Dora musu, ya kuma roki kwamatin, da suyi aiki da lura da Gaskiya.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: