DA DUMI-DUMI: Za mu hukunta ‘Yan Shi’a a matsayin ‘yan Ta’adda

Rundunar ‘yan sanda ta kasa, ta fitar da sanarwar cewa, duk kan wasu shirye-shiryen tsohuwar kungiyar nan ta ‘yan uwa Musulmi haramtacce ne, kuma hiri ne na ‘yan ta’adda.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar jiya, ta bakin kakakinta DCP Frank Mba, yace hukumar ta ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda ta kuma haramta kungiyar tun daga ranar 26 ga watan Juli na wannan shekarar.

Saboda haka hukumar take sanar da cewa, duk wani yunkuri ko motsi na kungiyar, harantacce ne, kuma hukumar ‘yan sanda za ta dauki matakin hukunta duk wadda ta kama a matsayin Dan ta’adda.

Jairdar Daily trust tace, kakakin na ‘yan sanda, yace, Shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa, ya baiwa shugabannin ‘yan sanda na jihohi da mar fita ran gadi da kuma tabbatar da cewa ‘ya’yan wannan haramtacciyar kungiya ba suyi wani motsi ba.

Masu Alaƙa  ‘Yan Shi’a sun kashe DCP Umar Usman tare da cinnawa motocin ‘NEMA’ wuta

Shugaban yayi kira ga al’umma da su sanar da hukumar duk wani motsi ko takurar wa ta ‘yan wannan haramtacciyar kungiya. Kana ya ja hankalin iyaye da su lura da yaran su, a wannan haki da ake ciki.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: