(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Gwamnatin Kaduna ta shirya yiwa Dawakai 1000 allular rigakafin kamuwa daga Zazzabin Dabbobi

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Kaduna tace nan bada jimawa ba, zata fara yiwa Dawakai 1000 allular rigakafin kamuwa da cutar Zazzabin Doki.

Daraktan kula da lafiyar Dabbobi dake karkashin Ma’aikatar Noma, Samuel Tanko-Dogo, ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’.

Sameul Tanko yace za’ayi wa Jakuna 314 rigakafin kamuwa daga Zazzabin Dabbobin.

Ya bayyana cewa gwamnatin ta dauki matakin yin allurar rigakafin ne domin yakar cutar Zazzabin Dabbobin da ta barke a jihar tin a watan Janairu.

Cutar Zazzabin na Dabobbi ‘Equine Influenza Virus’, cuta ce dake kama bangarorin numfashin Dawakai da Jakuna.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog