Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Gidauniyar wasu ‘yan mata a Kano ta kai tallafin kayan abinci da tufafi zuwa gidan marayu da gidan yari

1 min read

Gidauniyar Hadeeyatul Khair da wasu mata a jihar Kano suka kafa ta kai tallafin kayan abinci da tufafi zuwa gidan marayu da gidan yari a jihar Kano.

A ranar 7 ga watan Julin 2019 ne dai gidauniyar ta kai ziyararta ta farko zuwa gidan Marayu dake Nassarawa a jihar Kano, inda suka rarraba kayan abinci, kayan sakawa dama daffafen abinci domin ciyar da mazauna gidan.

Kayayyakin sun hadar da Sabulan wanki, Sabulan wanka, Madara, Biskit, Chizi, Lemuka da Gurasa.

Wasu daga cikin kayyakin da Gidauniyar ta rarraba.

Duk dai a ranar 7 ga watan Juli, Gidauniyar Hadeeyatul Khair ta kai ziyarar tallafin zuwa gidan yari dake Goron Dutse ta jihar Kano.

Yayin Ziyarar Gidauniyar zuwa gidan yari na Goron Dutse, Kano

Shugabar hulda da jama’a ta gidauniyar, Pharm Rukayya Kabir Abbas ta bayyanawa DABO FM cewa sun kafa gidauniyar ne domin bada tasu gudunmawar ga tallafawa marasa karfi da niyar rage musu radadin da zafin rayuwa.

Yayin ziyarar Gidauniyar zuwa gidan Marayu dake Nassarawa, Kano

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.