(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Duk wata rigima da akeyi a Kano akwai hannun Abdullahi Abbas a ciki – Hon Abdulmumin Jibrin

dakikun karantawa

Hon Abdulmumin Jibrin, dan majalissar tarayyar mai wakiltar karamar hukumar Bebeji/Kiru, ya bayyana Abdullahi Abbas, shugaban jami’iyyar APC na jihar Kano, a matsayin musabbabin dukkanin wata rigima da akeyi a jihar Kano wacce ta shafi Siyasa dama wacce bata shafa ba.

Hon Jibrin yayi wannan furuci ne yayin wata ganawarshi da manema labarai da yayi a garin Abuja biyo bayan wata kura data kunno kai tsakanin shi da Abdullahi Abbas.

A Kano gaba daya, duk inda kaga wata matsala a jami’iyya, ko rigima bata shafi jami’iyya ba gaba daya, kaje kabi diddigi ka gani, kayi bincike, duk Abdullahi Abbas ne.”

DABO FM ta binciko cewa Hon Abdulmunin Jibrin ya kara da cewa duk wanda yake ganin maganar da yayi ba haka take ba, to babu shakka zai iya nemanshi domin ba bashi hujjojin maganarshi.

Ni kuma na yadda cewa duk mutumin da yake ganin wannan maganar ba haka take ba, a shirye nake in zauna dashi in bashi hujjojina na cewa duk wata rigima da kagani yau a Kano, akwai hannun Abdullahi Abbas. Ko dai shine ya kirkiro rigimar ko kuma shine yake saka wuta baya so a daina.

DABO FM ta binciko cewa rikicin ya bullo ne bayan da Hon Abdullahi Abbas yayi yunkurin kafa kwamiti domin hukunta wasu ‘yayan jami’iyyar APC na karamar hukumar Bebeji da yake zargi da yiwa jami’iyya zagon kasa bisa dalilin rashin zuwansu taro da Abdullahi Abbas ya kira.

Abdulmumin Jibrin ya zargi Abdullahi Abbas da assasa sauke wadansu ‘yayan jami’iyyar APC a karamar hukumar Bebeji daga mukamansu wanda a cewarshi yace sune masu jama’a.

“An bi duk inda muka saka mutane a gwamnati, gaba daya aka je ana ciresu, shugaban mulki ya bada sanarwar cire Sakataren mulki na karamar hukumar Bebeji wai don yaro na ne.

Ya bayyana cewa an cire “Center Officer” Kabiru Kofa, an cire su. Duk wadannan abubuwan duk Abdullahi Abbas ne yake yi, wasu wuraren shi yake yin waya yasa ayi.”

Saurari Sautin Muryar Hon Abdulmumin Jibrin

Karin Labarai

Sabbi daga Blog