Nasir Salisu Zango :Hikimomi 10, Akan gasar yiwa miji kara’in rawa.
1..Kusan dukkan matan da naga fefen bidiyon su kosassu ne ko kuma ‘yan Duma Duma, muciya da zani kwalli daya nagani a ciki
2.. Da yawan su gyatumai suka aura, kodai watakila sun yi wuf da iyayen wasu ne, la’ Akari da ganin cewar yawancin mazajen sun kwana 2,illa dai alamun karfin naira wacce ga alama ta karawa auren danko da da iskar Oksajen, Shiyasa yawancin mazan furfura ta gama yi musu wasali a jiki, kuma kaso 60 cikin 100 na mazan da aka shiga wannan gasa dasu, ba ‘yan nanaye bane, dattijai ne kawai da naira ta zaunawa da gindin ta, Dan haka a fefen bidiyon suke nuna alamun basu ma san sautin breka ba, balle su Mai da ta yin rawar da ake taka musu.
3..Kusan dukkan faya-fayan da suka fito, tsararru ne ma’ ana Sai da aka shirya sannan aka gabatar, wannan ya nuna cewar, akwai fardusa da darekta da kuma afta da aftress.kaga Kenan faya fayan sun cika wasu sharudda na wasan kwaikwayo wanda Hakan watakila yasa Afakalla ya Sami ikon shiga ciki yayi aikin sa idan har ba a kai masa ya tace ba.
4..An nuna salon maganar Bahaushe dake cewar komai na Babba yafi na yaro, domin dattijan cikin faya fayan basu taka rawa ba illa kallo da mamaki da suka yi duk da cewar su akayi WA rawar, in banda wani Mai ruwan farfesoshi da ya nuna shauki ya jingine Sanda ya shiga aka dama dashi, watakila wannan zai iya zame musu uzirin ba da yawun su aka yi ba, Koda zata kasance Afakalla ya shiga maganar tun da munce faya-fayan sun cika wasu sharudda na fim.
5…Kamar yadda na fada, Naira ta zauna a dukkan gidajen da aka yi wannan fina-finai na Hausa, Dan haka nake ganin kwanciyar hankali sanadiyar karfin masu gidan rana ya karawa gasar armashi, idan muka duba zamu ga kamar ma akwai warwarar jigo tun da Bayan babban jigo na yin rawa da nuna soyayya akwai karamin jigo na gasar nuna girman palo da tsadaddun kujeru da kilisai.
6…Idan ka cire ta farko Mai gwala-gwalai fal hannu yawancin wadanda suka shiga gasar sun shiga ne domin samun moriyar kyautar naira dubu 20, kamar yadda na ji madigar ajin ta bayyana.
7…Kamar akwai alamar an yiwa matan wayo domin ita shugabar ajin, Bata saki nata bidiyon ba duk da cewar ta cika sharuddan shiga gasar, tana da miji, tana da Kiba, tana da tankasheshen palo amma Sai ta tsaya daga baya, Koda yake watakila nata Sai a fadan karshe.
8…Kwararrun ‘yan wasan kwaikwayo 2, Saratu Gidado Daso da Rasheeda me sa’ a sun Sami sabani Akan wannan fim, Daso tace an yi daidai Rasheeda kuma tace an yi asara.
9..Malamai kuwa kamar Malam Ibrahim Khalil da Malam Abdusalam Baban Gwale sun yi ijma’i inda suka ce yin rawar laaba’asa, amma yadawa duniya laifi ne.
10…Gasar itace irin ta ta farko a tarihin kasar Hausa Dan Haka wadanda suka fara zasu Sami ladan fara aikin alheri idan abin ya halatta, idan ko ya zama ya haramta nan ma bazasu kasa samun kamasho ba, Amma fa ba’a shiga tsakanin Ubangiji da bawansa.
Kuma kuna iya Kara naku.
