Labarai Manyan Labarai

Saudiyya za ta bude masallatai 90,000 da aka rufe sakamakon Kwabi-19

Ma’aikatar addinin Musulunci ta kasar Saudiyya ta tsunduma cikin shirin bude masalallati sama da 90,000 a fadin kasar domin cigaba da gudanar da ibadu.

Hukumar tace tini ta fara wanke masallatan domin gudun kmauwa da cutar Kwabid-19 da ta sanya rufe masallatan kimanin kusan watanni 2.

Sai dai ma’aikatar tace banda masallatan garin Makkah a cikin wadanda za a bude a ranar daga ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2020.

Cikin labarin da wani gidan Talabijin a kasar ta fitar, yace a ranar Juma’a bayan an bude masallatan, za a rika bude masallatan Juma’a mintuna 20 kafin lokacin tayar da Sallah, hakazalika za a rufe masallatan mintuna 20 bayan idar da Sallar Juma’a.

Haka zalika gidan Talabijin na kasar ya rawaici cewar ranar Alhamis, kasar ta rage awanni dokar hana fita daga awanni 24 zuwa awanni 15 a kowacce rana.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kasar Saudiyya zata gayyaci Jay Z da Beckham, bude gidan rawa

Dangalan Muhammad Aliyu

CoronaVirus: Saudiyya ta bude Masallatan Makkah da Madina

Dabo Online

Coronavirus: Kasar Saudiya ta dakatar da zuwa aikin Umrah

Rilwanu A. Shehu

‘Yar Saudiyar da tayi ridda, ta samu mafaka a Canada

Dabo Online

Kasar Saudiyya ta bayyana ranar Asabar, 10 ga watan Agusta a matsayin ranar Arfah

Dabo Online
UA-131299779-2