Babban Labari Labarai

Dole kowa ya bada gudunmuwa domin cigaban kasa – Aminu Alhassan

Babban Jami’i mai kula da wayar da kan al’umma ta karamar hukumar Zariya a Jihar Kaduna, Alhaji Aminu Alhassan Sa’id, ya bayyana yadda bangaren su da ke da alhakin wayar da kan al’umma game da lamuran da ke faruwa a sassa daban-daban, musamman ma na halin da ake ciki akan cuta mai sarke numfashi ta Covid-19 a matsayin abun da ke taimakawa wurin wayar da kan al’umma a yankunan karkara.

Ya bayyan haka ne da yake tattaunawa da wakilin Dabo FM a Zariya.

Ya yaba ma gwamnati a kokarin da ta ke na samar da wasu muhinman dokoki musamman domin al’umma, sai dai a wasu lokutan akan fuskanci kalubale daga wurin wasu al’ummomin ta yadda sam ba su girma umarni ko shawarar gwamnati.

Ya kara da cewa, duk da Jama’a na cikin kunci, amma dole ne a sani fa hannu daya baya daukan jinka, Dole ne kowwa ya zo a hadu domin a hada karfi da karfe domin ciyar da Najeriya gaba.

Ya bada misali ga wasu muhinman ayyuka da suka yi a karamar hukumar Zariya, na shiga yankunan karkara tare da tara su kuma suna fadakar da su akan cuar Covid-19, kuma yanzu haka wannan shiri ya yi nisa inda suka shiga yankunan Dakace da Bizara.

Alhaji Aminu Alhassan, ya yi fatan al’umma su guji sanya siyasa a dukkanin manofofin gwamanti musamman bangaren kiwon lafiya.

Karin Labarai

UA-131299779-2