(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

IMF ta shawarci Najeriya da ta janye tallafin Man Fetur

Karatun minti 1

Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, ya baiwa Najeriya shawarar janye tallafin man fetur.

Sakatariyar IMF, Ms Christine Lagarde ce ta baiwa kasar shawara a matsayin hukumar, tace cire tallafin man zai baiwa Najeriya damar yin wadansu aiyuka masu amfani ga al’umma.

Ms Lagarde tayi jawabin ne a wani taron tattalin arzikin kasashen duniya wanda aka gudanar ranar Alhamis a birnin Washington DC na kasar Amurka.

Tace tallafin da gwamnatin Najeriya ke sawa na man fetur din yana kawo wa najeriya koma baya a fannin kudaden shiga.

Tayi nuni da cewa Najeriya ta kashe kusan dala Amurka tiriliyan 5.2 daga shekarar 2015.

Daga karshe ta gwamnatin zata iya amfani da wadannan kudaden wajen samawa ‘yan kasa Ilimi, Lafiya da samar da ingantaccen ruwan sha.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog