Jama’ar gari ne kadai suke mutuwa a harin Jiragen Sojoji a Zamfara

Majalissar Sarakuna da shuwagabannin gargajiya na jihar Zamfara sun bayyana cewa hare-haren da jiragen Sojoji suke kaiwa a jihar yana kashe mutanen gari ne kawai.

Majalissar tace harin baya taba ‘yan ta’addar a guraren da jirgin sojojin yakai hari a unguwanni guda 5.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa, Majalissar Sarakunan wacce Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahir yayi jawabi a madadin Sarakunan yace, hare-haren Sojojin bai taba wadanda akayi harin dan su ba.

TALLA

Yace rahotannin daga kananan hukumomin Zurmi, Tsafe, Gusau da Anka, sun tabbatar da cewa mutanen garin aka kashe ba ‘yan ta’addar ba.

Daga karshe Sarkin yayi magana akan abinda Ministan Tsaro, Dan Ali ya fada da cewa akwai sa hannun Sarakunan gargaji a rikicin Zamfara.

Masu Alaƙa  Za'a gudanar da Zaben kananan hukumomi ranar 27 a jihar Zamafara

Sarki yayi kira da a dena buya a cikin wayo, yayi kira ga Ministan da yayi gaggawar bayyana sunayen Sarakunan.

Madogara daga Jaridar The Nation Nigeria
%d bloggers like this: