/

Ina jin kamar na kashe kaina saboda ƙuncin da na ke ciki – Ummi Zeezee

Karatun minti 1

Tsohuwar shahararriyar ‘yar wasan kwaikwayo a masana’antar Kannywood, Ummi Ibrahim, ta bayyana cewar tana cikin rayuwar ƙunci.

Jarumar da aka fi sani da Ummi Zeezee ta ce a yanzu tana cikin rayuwar mai ƙunci da bata jin dadin komai, a cewarta lamarin ya kai maƙurar da ta ke jin kamar ta hallaka kanta.

Zeezee ta bayyana haka ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Asabar.

“A ‘yan kwanakin nan, ina rayuwa ne cikin ƙunci da baƙin cikin da har ya kai na ke tunanin kashe kaina. Amma dan Allah kada wanda ya tambayeni meyasa.”

“Addu’arku kaɗai na ke buƙata.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog