Buhari ya yi jimamin rasuwar Dangalan, ya bayyanashi a matsayin mutum mai tsari da ka’ida

Karatun minti 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna jimaminsa ga rasuwar gwarzon dan siyasa, daya daga Iyayen NEPU da PRP, Muhammadu Dauda Dangalan da ya rasu a ranar Asabar.

Shugaban ya fitar da sakon ta’aziyyar ta hannun mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu a ranar Asabar a birnin Abuja.

Ya ce; “Ya kasance daga cikin mutane masu da tsari da ka’ida kuma dan gaba-gaba a tafiyar Mallam Aminu Kano.”

Shugaban ya kara da cewa, “mutane irin su Dangalan suna da wuyar samu a siyasarmu ta wannan lokaci, siyasar da ake tafiyar da ita da tsarin da ba ya amfanar al’umma.”

Shugaba Buhari ya sake bayyana cewar; ” a lokacin da suke ganuwar siyasarsu, Dangalan da Aminu Kano sun nakalci siyasa a matsayin aikin rashin sonkai da saka al’umma a gaba a maimakon wata hanya ta tara dukiya cikin sauki.”

“A irin kalar siyasarsu, Dangalan da Aminu Kano sun saka kansu wurin yi wa al’umma aiki.”

Daga karshe shugaban ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu tasowa su yi koyi da irin halayen Alhaji Dauda Dangalan. Ya kuma yi addu’ar Allah Ya masa gafara tare da ba wa iyalansa, gwamnati da al’ummar Kano da Najeriya hakurin rashinsa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog