Masarautar Kano na shirin cefanar da Masallacin Idi don gina gidaje

dakikun karantawa
Sarkin Kano- Amin Ado Bayero
Sarkin Kano Ado Bayero

Masarautar jihar Kano karkashin Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ta yi kunnen ƙashi ga umarnin da wata babbar kotu a Kano ta bayar na dakatar da masarautar daga cefanar da filin masallacin Idi na ‘yar Akwa.

Ana zargin masarautar za ta tsattsaga filayen domin ta siyar a yi gidajen zama a unguwar.

A ranar 2 ga watan Fabarairun 2021 ne dai al’ummar unguwar Darmawa da ke karamar hukumar Tarauni a jihar Kano ƙarƙashin ƙungiyar Darmanawa Layout Development Association, DALDA, ta yi bore ga matakin iyalan marigayi Alhaji Ado Bayero a kan yunƙurinsu na ‘kwace’ filin ƙarƙashin Ado Bayero Royal City Trust Fund, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce tana yi kan Sarkin Kano da wasu muƙarrabansa a kan badaƙalar cefanar da wasu filaye da kudinsu ya kai Naira biliyan 1,295,000,000 ba bisa ƙa’ida ba.

Da ya ke magana da manema labarai a ranar Asabar, shugaban kwamitin kula da filin idin, Tijjani Yahaya, ya ce sun cika da mamakin yadda su ka wayi gari da safe su ka ga motocin ‘yan sanda guda 5 su na kare wasu mutane da suke tsattsaga filin duk kuwa da umarnin da kotun ta bayar.

Ya bayyana cewar Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya mallaka wa al’ummar yankin filin domin a rika gudanar da Sallar Idi a ciki.

A cewarsa, a shekarar 2019, ƙungiyar ta miƙa ƙorafinta ga hukumar kula da filaye sakamakon wani yunkuri da su ka ga an yi na taɓa filin, filin da ya ce shi kaɗai ne filin idi a yankin na ƙaramar hukumar Tarauni a birnin Kano.

Kazalika ya ce basu daɗe da zuwa wajen mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ba domin nuna rashin gamsuwa da yadda ake yunkurin karɓe filin a ƙarƙashin Ado Bayero Royal City Trust Fund, wata hukuma da ke ƙarƙashin Masarautar Kano.

Ya ce Sarkin ya nemi da dukkanin bangarori su zama masu wanzar da zaman lafiya tare da  bayar da umarnin yin bincike a kan lamarin.

“Ƙungiyarmu ta sake shigar da ƙorafi zuwa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a watan Oktobar 2020. A yayin da muke jiran jin sakamakon ƙorafe-ƙorafenmu, wakilan Ado Bayero Royal City Trust Fund su ka yi yunkurin kwace filin ta karfi sai dai mun yi nasarar hana hakan a ranar 30 ga Disambar 2020.”

“A don haka, muna ƙalubalantar Ado Bayero Royal Trust Fund da su kawo wata shaidarsu ta mallakar filin idin, filin da ya ke na jama’a, kamar yadda Hukumar Tsarawa da Cigaban  Burane ta Jihar Kano ‘KNUPDA’ da lamba TP/UDB/18.”

DABO FM ta tattara cewar, shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa, a yunƙurin da su ke yi tabbatar da filin a matsayin na al’umma tare da kare filin daga masu son kwacewa, sun sake tuntuɓar Masarautar Kano domin yi mata tuni a kan korafin da suka shigar.

A cewarsa Masarautar ta yi burus har da turo jami’an tsaro domin su zaman garkuwa ga ma’aikatan da aka turo su sassare bishiyoyin filin a ranar Litinin 1 ga watan Fabarairu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog