Jami’ar KUST Kano ta dakatar da ɗalibai 10 da su ka ci zarafin ɗaliba mai sanye da Abaya

Karatun minti 1

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano ‘KUST’ ta dakatar da ɗalibanta 10 da aka samu da hannu a cin zarafin wata ɗaliba.

Hukumar ta ce kuma tana cigaba da gudanar da bincike, ta sanya gobe Alhamis a matsayin ‘Ranar Abaya’.

Shugaban kungiyar tsofaffin ɗaliban jami’ar, Suhailu Sabo Maccido ne ya tabbatar da lamarin a yayin zantawarshi ta wayar tarho da Jaridar Sahelian Times.

Kazalika shugaban ɗaliban jami’ar, Kwamared Uwaisu Ibrahim Babba, ya tabbatar da dakatar da jami’ar da yi wa ɗaliban su 10.

..

Karin Labarai

Sabbi daga Blog