Shekau ya kashe kansa yayin tsere wa kwamandojin ISWAP

Karatun minti 1

Shekau ya kashe kansa tare da wasu kwamandojin ƙungiyar ƴan ta’addan ISWAP bayan sun chafke shi.

Rahoton da yake isowa Dabo FM yanzunnan ya bayyana shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi ƙunar bakin wake tare da wasu cikin shugabannin ƙungiyar ƴan ta’addan ISWAP bayan sun kamo shi.

Jaridar HumAngle da wani gogaggen dan jarida da ke da kusanci da ƙungiyar, Salkida sun tabbatar da afkuwar al’amarin.

HumAngle ta bayyana cewa ƙungiyar ISWAP tasha kai kawo kafin ta chafke Shekau, wanda bayan an kashe mutanen sa ya miƙa kansa, daga nan aka shiga tattaunawa sa’o’i domin ya yi mubaya’a ga ISWAP.

Rahoton ya bayyana cikin wannan tattaunawa ne Shekau ya tada nakiyar sirri dake dauke cikin rigar garkuwarsa.

Tun a Laraba ne dai tsohon kakakin rundunar sojin ƙasa, SK Usman ya fidda sanarwar Wasu rahotanni da basu gama tantancewa ba sun bayyana cewa ƙungiyar ƴan ta’addan ISWAP sun kashe shugaban na Boko Haram.

Sai dai shakkun galibin al’ummar ƙasar bai wuce wannan shine karo na 4 da ake ikirarin mutuwar ta Abubakar Shekau ba. Da kuma fargabar ƙungiyar ta’adda ta ISWAP na iya zamu abin tsoro ga Najeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirka.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog