An sace ɗaliban Islamiyya su 200 a jihar Neja

Karatun minti 1
"Yan BIndiga

‘Yan bandiga sun sace ɗaliban makarantar Islamiyya ta je ka ka dawo su 200 a garin Tegina da ke ƙaramar hukumar Rafi a jihar.

Wani mazaunin yankin, Zayyad Muhammad ya tabbatar wa Sahelian Times faruwar al’amarin.

Rahotanni su bayyana cewa ‘yan bindgar sun sace ɗaliban a makarantar Islamiya ta Saleh Tanko da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi.

A yayin harin ta’addancin, an harbi mutum guda har lahira, dayan kuma yana can rai a hannun Allah.

Har kawo yanzu, rundunar yan sanda ba ta ce komai a kan faruwar al’amrin ba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog