(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kajuru: ‘Yan Bindiga sun kashe mutum 21 tare da yin awon gaba da Shanu 50 a Kaduna – ‘Yan Sanda

Karatun minti 1
"Yan BIndiga

Rundunar ‘Yan Sanda reshen jihar Kaduna tace wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 21 tare da awon gaba da Shanu 50 a kauyen Ungwan Aku dake karamar hukumar Kajuru,  jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar, Yakubu Sabo, ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya bayyana cewa mutum 21 sun rasa rayukansu bisa harin da ‘yan bindigar suka kawo unguwanni 2 a Kajuru.

Yakubu yace a lokacin harin, an samu raunuka 3 na harbin bindiga tare da lalata gidaje 10.

Ya kara da cewa, ‘Yan bindigar sunyi awon gaba da Shanu 50 bayan sun gama harbe-harben.

‘Yan bindigar sun kai hari a kauyukan Banono da Ugwan Aku duk dai a karamar hukumar Kajuru.

Ya dai ce ‘Yan bindigar sun shiga garin ne a kan babura inda suka fara harbin mai uwa da uwa a cikin kauyukan.

A takardar sanarwar da rundunar ta fitar ranar 08/04/2019, ta bayyanawa cewa ta samu kira inda aka sanar da ita shigar ‘yan bindigar cikin kauyukan.

“Maharan sun fara harbi kan mai uwa da wani, sun kashe mutane 21, sun jikkata mutane 3 tare da lalata gidaje 10.”

Ya kara da cewa rundunar ta samu kai agajin gaggawa inda ta hada jami’anta, dakarun Soji hadi da ‘yan sintiri domin kai dauki garin, yace sun samu yin artabu dasu.

Yanzu haka rundunar da kai wadanda aka raunata asibit domin karbar taimako.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog