Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Gobara a KANNYWOOD: Hadiza Gabon ta mammari Amina Amal, bisa zarginta da neman yi mata lalata

3 min read

Shahararriyar kuma fitattaciyar jaruma a Kanywood, Hadiza Ali Gabon, ta mammari Jaruma Amina Amal.

Hakan na zuwa bayan da Amina Amal ta wallafa a shafinta na Instagram cewa, Hadiza Gabon na nemanta da aikata masha’a.

Daga nan ita Hadiza Gabon ta harzuka wanda har tayi kokarin ta iske Amal da kanta.

Faifayen bidiyo dayawa sun fara fitowa jim kadan bayan nuna fushin Gabon akan zargi.

An dai hangin Gabon din ta titsiye Amal tana mata tambayoyi kamar haka:

Hadiza Gabon: Amina, na taba cewa Ina sonki? , na taba jn zan neme ki na iskanci?

Amina Amal: A’a

Hadiza Gabon: To meyasa kikamin sharri?

Amal: Kiyi hakuri sharrin Shaidan ne.

Gabon: Sharrin shaidan ne ko na kwaya?

Latsa alamar “Play” domin kallo.

Daga daya faifan bidiyon kuma, an hangi jaruma Hadiza Gabon tana marin Amal tare da bata umarni ta karanta “Chat” din da sukeyi da ita.

Rikici ya samo asali ne a daidai lokacin da Amal ta wallafa wani hoto da yayi kama dana batsa a shafinta na Instagram, wanda yaja hankalin su kansu ‘yayan masana’antar Kannywood, inda sukayi mata cha akan cewa ta cire hoton don bai dace ba.

Latsa “Play” domin sauraro.

Itama Hadiza Gabon ta tsoma baki a kan maganar hoton, inda tace

“Ke wawuyace banza Wallahi azim, kuma wannan abin da kike bashi zaisa kiyi suna ba.”

(GH)Wannan shine hoton da Amal ta wallafa.
(DK) Martanin Gabon akan hoton.

Bayan nan ne ita Amal ta kufula, ta fara mayar da martani kakkausa, tana nuni da cewa ita dai bata neman mata, kuma tanada hujjar da aka nemeta wacce aka nemi kada ta fadawa kowa.

Martanin Amal ga Gabon. Hoton da tace sunyi magana da Gabo a Instagram

“Kuma ni bana c*n mata, sai sai ace ina shigar da bata dace nnnbnba. Duk wanda yace ni Karuwa ce, baida hujja sai dai ace yanayin shiga ta. Idan na kara wallafa wani abu a shafina kika zageni, wallahi sai na fadawa duniya kema ‘yar iska ce.

Har yanzu ina ganin girmanki, amma in baki ja girmanki ba to lallai bazan cigaba da mutunta ki ba.

Kiyi harkar ki kawai, kuma har yanzu inada maganganun da mukayi dake na sirri.

Ki dena buya a bayan wayonki, karki kara zagi na in ba haka ba kuma zaki sha mamaki.

A nasu bangaren, wasu daga cikin jarumawan da suka tsoma baki a maganar, Nafisa Abdullahi, tace bai ita Hadiza tayiwa Amal din haka ba, ta bari duniya tayi mata shaidar rashin laifi, ba ta dauki doka a hannun ta na dukan Amal ba.

Tsokacin Nafisa Abdullahi

“Ke kina Kokarin kare naki mutuncin amma ke sa kanki kina kokarin nunawa dubiya laifin ta. Idan da kowa yana bin wannan hanyar, to ke ma bazaki tsira ba.”

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.