Taskar Malamai

Kano: Har Bature ya gama shegantakarshi a Najeriya, bai yi abinda muke gani yanzu ba – Sheikh Dahiru Bauchi

Fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman ya magantu akan rikicin daya barke tsakanin tsagin gwamnatin da masarautar jihar Kano.

Sheikh Bauchi ya magantu da cewa lallai abinda ya faru a Kano na raba masarauta, abin tsoro ne ga mutane, domin ita jihar Kano, jiha ce ba gama garin jihohi ba.

“Abin da ya faru (A Kano) ya tsoratar da mutane, Bature ya ci kasar nan (Najeriya), ya mallaki kasar, har ya gama shegantakarshi da shekara 60 bai taba masarautar Kano da sunan wargazawa ba.”

Majiyar Dabo FM ta rawaito cewa; Sheikh Bauchi yace tin sanda aka fara mulki a jihar Kano da Najeriya, Sarakuna da masu mulkin siyasa, babu wanda yayi wa Kano abinda ake mata yanzu ba.

“Wadanda sukayi sarauta da mulki, anyi gwamnati wajen kusan gwamnati 9 na sojoji, 7 na fafar huila a Kano, amma ba wanda ya tunkari Kano da irin wannan abinda ake tunkartar ayi yanzu, domin Kano ba irin sauran jihohi bace, zan nanata. “

Sheikh ya kara da cewa; yayi niyyar yiwa mutanen jihar Kano jajen abinda ya faru, amma bayan ya samu labarin ruguje Sarakunan da Kotu tayi, yayi farin ciki da jin lamarin.

Karin Labarai

Masu Alaka

Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, namijin jiya, ‘an rasa har yau ana mora’

Dangalan Muhammad Aliyu

Allah Ya’azurtani da samun ‘Ya’ya 70 da tarin Jikoki – Sheikh Dahiru Bauchi

Dabo Online

Yunwa, Talauci, Tashin hankali da bala’i kawai ake fama dashi a Najeriya – Sheikh Muhd Nasir

Dabo Online

Gwara dan Ak*yar da zai ga mutane ya kauce hanya ya basu wuri – Sheikh Abdullah Gadon Kaya

Dabo Online

Zagin Shuwagabanni da Malaman Addini tamkar zubar da jini ne – Dr Rijiyar Lemo

Dabo Online

Dabi’un Musulmi bisa koyarwar Manzon Allah S.A.W, Daga Mal. Aslam Bin Uthman

Dabo Online
UA-131299779-2