(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Gwamnan Zamfara ya rike albashin ma’aikata 1,400 na tsawon watanni 30

dakikun karantawa

Ma’aikata 1,400 da gwamnatin jihar Zamfara da dauka aiki tin shekarar 2014, sun bukaci gwamnatin ta biya su hakkin su na albashin watanni 30 da suke bin gwamnatin.

Ma’aikatan da gwamnatin ta dauka tin watun Mayun shekarar 2014, sun bayan hakane a wani taron manema labaran da suke gudanar a yau Alhamis, ma’aikatan da shugaban kungiyarsu, Lukman B Majidadi yayi jawabi a madadinsu yace; a cikin wadannan shekaru 5 da aka shafe, mafiya yawancinsu suna rayuwa ne a cikin kunci da takura bayan da gwamnatin da dauki matakin wulakanta su.

 “Bayan an dauki lokaci anata tantancewa mai tsanani,  an ware wanda gwamnatin ta aminta dasu ma’aikata 1,400 daga cikin 8000 wandanda ta yadda ta daukesu yin aiki a karkashin ta.”

“An raba takardun shaidar daukar aikin na mutum 1,400 da aka tantance, sai dai tin daga wancen lokacin, ko sisin Kobo basu bamu ba.”

 “Tinda har ba’a bamu takardun sallama daga aiki ba, to lallai muna daga cikin ma’aikatan wannan jihar, kuma dole ne a biyamu dukkanin hakkokin mu.”

 “Sai dai muna ganin ana mana haka ne saboda tin farkon daukar mu aikin, bamu aka so a dauka ba, bayan tantancewar da akayi mana, duk aka zubar da wadanda suke so.”

Ya kara da cewa; mafi ya yawancinsu Malamai ne, Lauyoyi, Ungozomomi da Akantoci, amma duk da haka ya rage masu babu wani zabi face wasun su su fara sana’ar tuka babur mai kafa 3, da jiran shaguna domin cigaba da gudanar da rayuwarsu domin “Mun fito ne ba daga gidan hannu da shuni ba.”

Bayan an tuntubi shugaban ma’aikata jihar, Alhaji Muhammad Mujtaba Isah, yace ba’a saka ma’aikata 1,400 a jadawalin biyan albashi bane, saboda wasu matsaloli da suka faru tsakani ma’aikatar kudi da kwamitin da ya dauke su aiki.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog