Nishadi

Kotun ta bawa CP Wakili umarnin kama Hadiza Gabon

Wata babbar Kotu a jihar Kano ta baiwa rundunar ‘Yan sandan jihar Kano umarnin kame fitacciyar jarumar wasan Hausa , Hadiza Gabon.

Kotun ta bada umarnin ne biyo bayan kin mutunta umarnin Kotun da Hadiza Gabon tayi.

Tin dai 15 ga watan dayta shude dai, Jarumi Mustafa Nabruska ya shigar da kararshi kai tsaye zuwa ga Kotu.

“Majiyoyi sun tabbatar da cewa Nabruskan ya dauki matakin kaiwa Kotu bisa cewa ‘yan Sanda bazasu dauki matakin kamata ba.

Wani jarumi daya bukaci a sakaya sunanshi, ya shaidawa Daily Nigerian cewa;

“Hadiza Gabon tana da mutane da abokai, musamman a cikin ‘yan sanda da wasu manyan yan siyasa.”

A ranar Alhamis, Mai shari’a Justice Muntari Dandago ya umarci kwamishan ‘yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili ”SINGHAM” da ya kamo jaruma Hadiza Gabon.

“Tinda wacce ake kara ta bijirewa umarnin Kotu na kawo kanta, to na umarci kwamishan yan sandan jihar Kano, Wakili ya kamo ta.”

“Na kuma umarci Kwamishinan da yayi bincike, kuma ya hukunta wacce ake karar idan an same ta da rashin gaskiya tin kafin a dawo gaban Kotu.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Gobara a KANNYWOOD: Ali Nuhu ya kai karar Adamu A. Zango Kotu bisa tuhumarshi da batancin suna

Dangalan Muhammad Aliyu

Yadda jaruman Kannywood suke taimaka wa yaduwar labaran bogi

Dabo Online

Zamani Riga: Me duniyar Kannywood take ciki a Yau da nasarorinta?

Dabo Online

Buhari bai bawa dan Fim din Hausa, Nura Hussaini mukami ba

Dabo Online

Shekaru biyar da rashin Dan Ibro: Waye ya maye gurbinshi?

Dabo Online

Har yanzu matsayin Jarumawan Arewa bai kai a nuna wa duniya ba – Naziru Ziriums

Dabo Online
UA-131299779-2