Labarai

Kwankwaso ya jagoranci ƙaddamar da yaƙin neman zabe.

Mai girma sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano Engr Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya jagoranci

 ƙaddamar da yaƙin neman zabe na jam’iyyar PDP na kano ta arewa a karamar hukumar Bichi. Taron wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar ta PDP ciki harda dan takarar ta na gwamna Engr Abba Kabir Yusuf.

Sanatan ya jajentawa al’ummar yankin akan aiyuka daya fara a lokacin da yake gwamnati amma gwamnatin jihar ta yanzu ta watsar dasu. Sanatan yayi ta fado aiyukan daban daban wanda gwamnatin yanzu ta gaza akai, fannin ruwan famfo, makarantu na sakandire dama na gaba da sakandire.

Daga karshe kuma sanatan yayi kira ga al’ummar yankin dasu yi zabe cikin lumana babu tashin hankali.

 

Karin Labarai

UA-131299779-2