Dabo FM ta kaddamar da fara shirye-shirye.

dakikun karantawa
dabo fm

Bayan dakatar da fara shirye-shirye da tashar DABO FM da ake gabatarwa a shafin Intanet tayi, tashar ta dawo aiki bayan taron kaddamar wa da aka gabatar a kasar Indiya.

Ranar Juma’a 21/12/2018,  shugaban sashin gudanarwa, Muhammad Aliyu Dangalan ya jagoranci fara shirye-shirye.

Taron ya samu halartar mutane daban daban wadanda suka hada da Mal. Ibrahim Haruna Luda babban ma’akaci a asibitin Specialist dake jihar bauchin Najeriya, Mal. Muhammad Yusuf Baba Madugu (Bauchi), Abdullahi Muhammad Saleh (MLT) (Bauchi), Yusuf Abubakar Kama (Adamawa), Ibrahim Sa’idu Noboi (Adamawa) da Mal Muhammad Auwal daga jihar Gombe.

A jawabin shugaban, Muhammad Aliyu Dangalan ya bayyana jin dadinshi na yadda mutane suka amsa gayyata domin kaddamar da fara shirye- shiryen.

“Bismillahi rahmanirrahim, Ina yi wa Allah godiya da ya nuna mana wannan rana mai cike da tarihi, ranar da Allah ya bamu ikon tabbatar da abinda muka dauki dogon lokaci muna fatan fara yi. Wannan kafa mai suna DABO FM kafa ce wacce muka kafa domin wayar da kan al’ummarmu musamman matasa a kan matsolin da muka dade muna fuskanta ta fannin zamantakewa dama sassan rayuwa. Muna da shiri na bullo da hanyar karatu a sauƙaƙe domin sadar da matasan mu ga yanar gizo gizo. Za a iya sauke manhajarmu a Google Play Store, ga masu wayar andriod domin sauraro, ko kuma a manhajar Radio.net ga masu Iphone.”

“A baya mun fara gabatar da shirye-shirye kafin daga bisani muka dakatar sakamakon wasu matsaloli, cikin ikon Allah yau mun sake dawowa wanda a yanzu muke fatan Inshaa Allahu, mun bude kenan. Muna fatan za a cigaba da bamu gudunmawa.”

Haka zalika shugaban ya sanar da fara aikin shafin yanar gizo-gizo da za a rika wallafa labarai da sauran shirye-shirye tare da bude bangaren karatu ga dalibai musamman na lafiya.

“Ina sanar da cewa mun kammala bude shafinmu na yanar gizo, wanda dama yana aiki, za a iya samunshi a www.dabofm.com. Yanzu haka akwai bangaren karatu da muka saka wasu karuttukan lafiya ga dalibanmu.”

Sauran mahalrta taron da suka yi jawabi, Mallam Ibrahim Haruna Luda sun bayyana jin dadinsu bisa nasara da suka ce DABO FM ta samu.

Gaskiya naji dadi kuma nayi farin ciki da bude wannan gidan rediyo da yara matasa yan arewa suke kokarin sadarwa. Musamman shirin da mukaji na wayar da kan matasa, kuma yakamata ku riƙa fada musu cigaban da kuka ganin anan. –Mal Ibrahim Haruna Luda

Wanann rediyo tana ilmantar da mutane akan zamantakewa musamman bangaren matasa da ma zamantakewar aure. Muna godiya da wannan gayyata da aka mana.Mal. Yusuf Baba Madugu

Yau ranar farin ciki ce sosai ce sosai ace an gayyace ka kazo kaga abinda dan’uwanka matashi yayi. Wannan radio tana kawo shirye shirye na matasa gaba daya kuma yau ace matashi ɗan’uwanka yana kawo abu na wayar da kan al’umma. – Yusuf Abubakar Kama.

Daga karshe ina muku godiya da kuka samu damar halatar wannan taro kuma muna fata zaku sanar da abokai da kuma yan uwa. Allah ya taimakemu ya bamu iko cigaba da wannan babban aikin da muka dauko.

Anyi wannan taro ne a kasar garin Jaipur dake arewacin kasar Indiya a jihar Rajasthan.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog