Malamai miliyan 1 na kasar Kanada sun nada Sarkin Kano shugaban kwamitin ‘Mashawarta’

Malamai miliyan 1 da sukewa kansu lakabi da sunan 1MT, sun nada sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II a matsayin shugaban kwamitinsu na mashawarta a Najeriya.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, an sake nada Sarkin na Kano a cikin kwamitin iyaye na kungiyar ta malaman guda miliyan 1.

DABO FM ta binciko Babban shugaban zartawa na 1MT, Hakeem Subair, ya bayyana nadin Sarki Muhammadu Sunusi II a matsayin gagarumar nasara ga gamayyar malaman suka samu tare da kara samun hubbasa wajen tafiyar da ayyukansu.

Ya kara da cewa, 1MT ta kasance mai neman muryoyi masu karfi, wadanda zasu taimaka musu wajen kara musu kaimi domin tafiyar da aikinsu tare da zama tudun dafawar kwamitin.

“Tare da matukar farin ciki da girmamawa, muna yiwa mai Martaba, Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, barka da zuwa a matsayin shugaban kwamitin mashawarta na gamayyar malamai miliyan (1MT).

Shi ma a nashin bangaren, mai martaba Sarkin Kano, ya bayyana cewa zai aiki da su domin cigaba da ayyukan da malaman sukeyi wajen samar da malamai ingatattu a fadin duniya musamman a kasasen yammacin Africa.”

“Naji dadi matuka akan shirin da gamayyar Malamai take shirin yi wajen inganta Ilimi na Najeriya.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.