Siyasa

Burin Shuwagabanni ne ‘ya ‘yan Talakawa suyi ta yi musu wahala su da jikokinsu – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa buri ne a wajen shugabanni Najeriya musamman na Arewaci, su ga ‘ya ‘yan Talakawa suna samun cigaba a rayuwarsu.

DABO FM ta tattaro cewa, Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a yayin wata tattaunawarshi da wasu gidajen Rediyo a jihar Kano.

Kwankwaso, ya yi tsokaci game da cigaba da a cewarshi suke samu a shari’ar su wacce suke kalubalantar nasarar da gwamna Ganduje ya samu a zaben da aka kammala a watan Maris 2019.

Ya jadda cewa suna nan suna saka rai domin “Gaskiya bata gushe wa” tare da saka rai da suke yi na samun nasara duba da irin yacce shari’ar take tafiya.

DABO FM ta tattaro cewa; Kwankwaso ya magantu akan shirin da gidauniyar Kwankwasiyyar take yi na tura ‘ya yan Talakawa 370 zuwa kasashen waje.

Ya bada tabbaci na cewa shirye-shirye sunyi nisa, “Wasu daga ciki mun sama musu guraben karatu, wasu mun kammala sama musu takarda daga ofishin Ilimi da shaida daga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Kano: Kwankwaso, Atiku zasu iya amfani da filin wasa na Sani Abacha – KNSG

Dangalan Muhammad Aliyu

Zaben Gwamna: Kwankwaso yaci akwatin kofar gidanshi

Dabo Online

Siyasar Kano sai Kano: Daga gobe kowa ya cire jar hula sai bayan zabe – Kwankwaso

Dangalan Muhammad Aliyu

Kwankwaso zai iya biyan kudin makarantar dalibai 370 daga cikin kudaden daya karba a majalissar dattijai – Bincike

Dabo Online

#NigeriaDecides2019: Alamu sun nuna kifewar Kwankwaso, Saraki da Dino Melaye

Dabo Online

Zaben2019: ‘Yan daban APC sun afkawa tawagar Kwankwaso a Bebeji

Dabo Online
UA-131299779-2