Shugaban ‘Haramtacciyar’ kungiyar IMN ta Shi’a, Mal. Ibrahimul Zakzaky ya tashi zuwa kasar Indiya

Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wadda aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakazky zai tashi daga filin jirgin Abuja zuwa Indiya a yau din nan.

Shugaban kungiyar haramtacciyar kungiyar IMN ta Shi’a, Sheikh Ibrahimul Zakzaky ya tashi zuwa kasar Indiya domin duban lafiyarshi daga filin tashi da saukar jirage na Nmadi Azikwe dake garin Abuja.

Sashin Hausa na Legit.ng ya rawaito cewa; El-Zakzaky zai tafi Indiya tare da matarsa Zeenat inda za su nufi Asibitin Medenta dake New Delhi a kasar ta Indiya domin a duba lafiyarsu.

Wata majiyar IMN dake Kaduna ce ta sanar da wakilin Daily Trust wannan labarin inda ta ce, jagoran na IMN yanzu haka yana Abuja tare da jami’an tsaron DSS inda yake jiran tashinsu zuwa Indiya a wani karamin jirgin sama.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.