Ni ba sa’an Sunusi bane – Ganduje

Shashin Hausa na jaridar Premium Times ya rawaito cewa;

“Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shi ba sa’an Sarkin Kano Muhammadu Sanusi bane ko a tsarin dokar kasa.

Ganduje ya ce da shugaban karamar hukuma ya kamata yana sa-in-sa ba gwamna ba domin nan ne hurumin sa sannan daidai shi.

” Gyara ne da ci gaba muka kawo jihar mu. Muna so mu kusanto da mutane kusa da shugabannin su. Amma ba daukar fansa ba ko kuma bibiyar wani.

” Idan ma har zancen ake so a yi ay a karkashin shugaban karamar hukuma ya ke ba gwamna ba. 

” Idan ba dun-ba-dun ba, ay da shugaban hukuma ya kamata yake gani idan bukatan haka ya tashi ba gwamna ba domin gwamna ya yi masa nisa. Haka dokar kasa ta gindaya.

” Wannan masarautu da muka kirkiro za mu tabbata mun gyara su sannan mun daga darajarsu da martaba a Idanun mutanen jihar.

Ganduje ya ce mutanen jihar na murna da wannan mataki ya gwamnatin sa ta dauka.”

Premium Times Hausa

%d bloggers like this: