(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Sheikh Aminu Daurawa ya ajiye aikin Kwamandan Hisba na Kano

Karatun minti 1

Babban kwamandan hisbah na jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya ajiye aiki a hukumar a matsayinshi na kwamandan rundunar.

Malamin tare da wasu abokanshi sun bada sanarwar ajiye aikin a yammacin yau Juma’a.

Sheikh Daurawa ya bayyana haka ne a shafinshi na Facebook mai sunan Mal. Aminu Ibrahim Daurawa.

Alhamdu Lillahi

“Ni da abokan aikina, yau mun ajiye mukaman da mai girma Gov ya bamu, bisa wasu dalilai, da za a jisu nan gaba, muna yiwa Jihar Kano fatan alkhairi da zaman lafiya da ci gaba.”


SHAIK ABBA ADAM KOKI, SHUGABAN HUKUMAR ALHAZAI TA KANO.
SHAIK ABUBAKAR UMAR KANDAHAR, KWAMISHINAN DINDINDIN NA DAYA A HUKUMAR SHARIA TA KANO.
DR MUHAMMAD NAZIFI INUWA, KWAMISHINAN ZAKKA NA BIYU A HUKUMAR ZAKKA.
MUHAMMAD AMINU IBRAHIM DAURAWA, DAGA KWAMANDAN HISBAH.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog