Al’ummar jihar Kano na ta cece-kuce dangane da sabuwar sanarwar da hukumar Karota ta fitar na haramcin goyon babur mai kafa biyu a jihar Kano.
Sai dai dokar ba sabuwa bace, illa iyaka a wannan karon gwamnatin ta ce ta haramta goyon babur din ne a kafatanin jihar Kano maimakon yadda dokar take a baya na iya cikin birnin Kano.
Sakamakon tabarbarewar tsaro a jihohin dake makotaka da jihar Kano, gwamnatin ta ce ya zama tilas ta dauki matakin kare rayukan al’ummar jihar Kano.
A zantawar shugaban kungiyar Karota, Bappa Babba Dan Agundi ya yi da gidan rediyon Arewa, ya ce mutane sun banzatar da dokar wanda a yanzu mutane suna yin goyo iya san ransu a jihar Kano.
Ya kara da cewa duba da yadda ake kai hare-hare a kan babura, ya zamewa gwamnatin Kano dole ta sake jaddada haramcin dokar tare da fadadata zuwa dukkanin fadin jihar Kano.
