Home SiyasaGwamnatin Buhari: Yawancin masu kuka sun mance 4+4, Takwas kenan ba Biyar ba -Shehu Sani

Gwamnatin Buhari: Yawancin masu kuka sun mance 4+4, Takwas kenan ba Biyar ba -Shehu Sani

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Tshohon sanatan Kaduna, Kwamared Shehu Sani yaci gaba da caccakar gwamnatin jam’iyyar APC ta shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rahoton DABO FM ya bayyana Shehu Sani nayin wani kurman baki a yammacin ranar Alhamis, wanda ranar 14 ga Yuni ma saida tsohon sanatan ya aike da sako bayan ware biliyoyin kudi wajen feshin kwarin gonaki duk da rashin tsaro da ya addabi arewacin Najeriya.

A wancan karon dai Shehu Sani ya bayyana “Ku fara kashe ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, sai mutane su iya zuwa gona domin kashe kwarin gona.” Martani kan kudaden da aka ware wajen feshin kwarin gona.

A wannan karon cikin wani raddi da yayi domin wadanda suka fara direwa daga wannan tafiya da shugaba Buhari, Shehu Sani ya bayyana cewa “Yawancin masu kuka sun mance idan aka tara 4 da 4 zasu bada Takwas kenan ba wai Biyar ba.”

Jawabin na sanatan da ya fitar a shafinsa na sada zumunta wata tinatar wace ga masu koken koken sun gaji da gwamnatin saboda rashin tsaro cewa dai zuwa yanzu dai cikin shekaru 8 na gwamnatin dake kai 5 kawai aka ci.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00