(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Ku karbi tsintsiyarku, na dena yi – Sakon jigo a APC

Karatun minti 1

Jaipur, India (DABO FM) – Biyo bayan rikice-rikicen da suka barke tsakanin ‘ya’yan jami’iyyar APC da ta kai ga ficewar gwamnan daga jam’iyyar, wasu daga manyan ‘yan jami’iyyar a jihar suna ta ficewa.

Hakan na zuwa ne bayan da jami’iyyar tace gwamnan jihar, Godwin Obaseki bai cancanci tsaywa takara a jami’iyyar ba.

Cikin wata takardar ficewa daga APC da wani jigon a jami’iyyar, Injiniya Akemokue Lukman ya aike wa shugaban jami’iyyar na mazabar Etsako Easts, ya ce ya bar jami’iyyar cikin salo da aka bayyana a matsayin abin dariya.

Ya ce; “Ko kunsan Obaseki (Gwamnan Edo) da Shu’aib (Mataimakin Gwamnan) sun fice daga APC? To ku karbi tsintsiyarku, na daina yi.”

Takarda dai ta ja hankali masu amfani da kafafen safa zumunta musamman a shafukan al’ummar kudancin Najeriya.

A wani labarin kuma, Victor Gaidam ya ayyana kanshi a matsayin sabon shugaban riko na jami’iyyar APC a Najeriya, awanni kadan bayan uwar jami’iyyar ta ayyana surukin gwamnan Kano, Abiola Adeyemi Ajimobi a matsayin sabon shugaban riko na jami’iyyar sakamakon jaddada hukuncin dakatar da Adams Oshiomole da kotun daukaka kara tayi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog