Rikicin Zamfara: Wallahi abinda yake faruwa yafi karfin Shugaba Buhari – Sheikh Abdallah Gadon Kaya

dakikun karantawa
Shiekh Abdallah Gadon Kaya

Fitattacen Malamin addinin Islama, Shiekh Abdallah Gadon Kaya yace abubuwan da suke faruwa na kashe-kashe da akeyi a jihar Zamfara yafi karfin shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Da yake bayani a wani faifan bidiyo daya wallafa  a shafinshi na Facebook , Sheikh Abdallah ya bayyana abubuwa na rashin dadi da suke faruwa yanzu a Najeriya bisa son zuciya da neman duniya na wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa da kuma jagororin Arewa suke dashi.

“Akwai wadansu daga cikin manyan kasar nan, lokacin fadar sunansu bai yi ba amma na sansu, manya ne kuma ‘yan arewa ne. Akwi arzikin ma’adanai a Zamfara, don haka, su suke da hannu wajen diban wannan ma’adanai suna fita dasu  waje suna samun dukiya.”

Sheikh Gadon Kaya yayi kausasan kalamai inda har ta kai shi ya bayyana dalilan daya sa aka fara tada fitina a jihar Zamfara.

Bayanan da yayi sunyi nuna da kiran cewa babban dalilin tada fitina a jihar shine domin a dibi ma’adanai na jihar, har ma ya kafa misali da dajin Sambisa inda yace a saboda danyen mai da yake daji yasa aka fara fitintinu a domin a kautar da hankalin gwamnati waje sace albarka tun kasa.

Daga bangare guda kuma yace shugaba Muhammadu Buhari yanada masaniya akan duk abubuwan da suke faruwa a Zamfara, sai dai yace shugaba bashi da wani karfin da zai iya yin abu saboda al’amarin yafi karfinshi. 

“Shi shugaban Kasa (Buhari) da kuke gani, wallahi yasan wannan abin, amma wallahi yafi karfinshi, sai dai da taimakon wadansu.

“Idan ya tura Sojoji ko ‘Yan Sanda, suma sunada masu basu umarni. Cikin manyan Sojoji suma sunada son su sami kudi.”


Bidiyon Shiekh Abdallah Gadon Kaya

Sai dai al’umma da dama na ganin cewa shugaba Buhari shine yake da damar ko ikon da zai yi duk mai yiwuwa wajen dakile wadanann abubuwa marasa dadi kama daga Garkuwa da mutane, harbin kan mai uwa da wabi da saurarn al’amura da suka kasance suna neman gagarar kundila.

Al’ummar Najeriya dai na kufule da biris din da shugaba Muhammadu Buhari yake yi akan kisan kiyashin da ake yiwa mutanen Zamfara, inda yake nuna alhini karara bisa kashe wani dan jihar Legas da jami’an SARS suka harbe a makon da muke ciki.

Har ma wasu na ganin a yanzu, akwai wata kabila mafi fifiko a Najeriya, wacce ko tari dan ta yayi, gwamnatin tarayya zatayi kokari wajen rarrashi tare da hukunta duk wanda zai matsa musu.

Yanzu haka dai Shugaba Muhammadu Buhari yana kasar Jordan, inda ya amsa gayyatar Sarkin Jordan domin halartar taron tattalin arziki na duniya.

Inda kuma bayan kammala taron zai wuce birnin Abu Dhabi na kasar UAE domin halartar wani taron, kamar yadda fadar gwamnatin ta bayyana.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog