Labarai Najeriya

Rikicin Zamfara: Rashin adalci ne ace ban damu da kashe kashen Zamfara ba – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa akan kashe kashen da ke faruwa a jihar Zamfara.

Wannan shine karon farko da shugaba Buhari yayi furuci game da takaddamar dake faruwa a yankin.

Shugaban yace, “Rashin adalci ne ayi tunani cewa ban damu da abinda ke faruwa a Zamfara ba, ko ayi tunanin ban tabuka komai akai ba.”

“Bani da wata damuwa illa tabbatar da baiwa mutanen Najeriya kariya, yana daga cikin manya nauye-nauyen da suke kaina.”

Shugaba Buhari ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cigaba da aiki tare da jami’an tsaro wajen tabbatar da anyi adalci domin samun kwanciyar hankali a yankunan Zamfara dama fadin Najeriya.

Ya kuma alkauranta cewa, zai cigaba da bawa  jami’an tsaro duk wata gudunmawar da zata kara musu kwarin gwiwa.

Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da kar su siyasantar da lamarin da yake faruwa a Zamfara.

Daga karshe ya mika ta’aziyyar shi daya kira da mafi girma bisa kashe kashe da tashin hankula da suke faruwa a jihar Zamfara.

Jawabin Sugaban Kasar na zuwa ne dai dai lokacin da al’umma Najeriya suka nuna rashin jin dadinsu ga salon shugaban kasar bisa kashe kashen da akeyi a Zamfara. Inda suka ce Shugaban yayi burus baya cewa komai balle yayiwa iyalan da jama’ar Zamfara jaje akan rikicin.

An dai hangi ‘yan kasar ciki har da mazauna kasashen waje suna nuna tasu damuwar akan rashin daukar mataki da gwamnatin shugaba Buhari takeyi.

A wani bangare guda kuma, an jiyo malaman musulunci irinsu Sheikh Abdallah Gadon Kaya yana cewa abinda yake faruwa yafi karfin shugaba Muhammadu Buhari. Shima maganganun Sheikh Gadon Kaya sun janyo cece kuce, inda wasu ke ganin tinda malami yace yasan wadanda suke sakawa akeyin wannan kashe kashen, meyasa bazai fadi ko suwaye ba.?

Karin Labarai

Masu Alaka

Bama samun Wutar Lantarki sai kazo Daura – Masarautar Daura ta fadawa Buhari

Dabo Online

Shugaba Buhari ya dauki hanyar zuwa kasar Jordan da Dubai

Dangalan Muhammad Aliyu

Gwamnatin Tarayya ta ba da aikin Hanyar da akai shekara da shekaru ana nema

Rilwanu A. Shehu

Gwamnatin Zamafara zata dauki matsafa 1,700 domin tabbatar da tsaro

Dangalan Muhammad Aliyu

Tinda China da Indiya suka cigaba, babu abinda zai hana Najeriya ci gaba – Buhari

Dabo Online

Sai na kashe Buhari – Victor Odungide

Dabo Online
UA-131299779-2