Yacce ta wakana a Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass daga birnin Kano

Karatun minti 1

Tin jiya Juma’a 29 ga watan Rajab shekarar 1440 bayan hijiran Manzon tsira (SAW), aka fara gudanar da Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass a tsakiyar birnin Kano.

Taron da ake gudanar wa a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a jihar Kano, ya samu halartar al’umma musamman mabiya darikar Tijjani daga fadin Najeriya dama wasu sassan nahiyar Africa.

Malamai da dama sun samu halartar Mauludin cikin harda Sheikh Haruna Rashid Dan Almajiri Fagge da dai sauran manyan malamai na darikar Tijjaniyya.

Mun samu damar zantawa da Alkasim Muhammad Bello, wanda ya samu damar halartar taron, inda ya bayyana mana cewa lallai al’umma sunyi dafifi wajen halartar taron Sheikh Ibrahim Inyass.

“Taron da mutane suka gani, taro ne mai dalili, saboda wanda akayi taron domin shi, kowa yasani masoyin Manzon Allah (SAW) ne.”

Ku bibiye mu a shafinmu na facebook domin sauraran hirar.

A lokaci guda kuma, daga birnin Abuja, inda ake gudanar da makamancin wannan mauludi a babban birnin tarayyar Abuja, wanda Sheikh Dahiru Usman Bauchi yake jagoranta.

Wasu daga cikin bidiyoyin yadda aka gudanar da maulidin.

 

 

Latsa alamar Play domin kallon takaitaccen Bidiyo

Karin Labarai

Sabbi daga Blog