(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');
//

Sojojin Nijar sun kashe yan Boko haram 280

Karatun minti 1

Ma’aikatar tsaron kasar Nijar ta bayyana cewa dakarunta sun kashe mayakan kungiyar boko haram 280a iyakar su dake kudu maso gabashin Najeriya.

An kashe yan ta’addar da adadinsu yakai 200 a sumamen da akayi ta sama, inda aka kashe 87 da sojin kasa tin daga lokacin da aka fara gudanar da wannan aiki a ashirin da takwas ga watan Disambar shekara dubu biyu da sha takwas, cewar hukumar a wata sanarwa data fitar a wata tashar talabiji dake kasar ta Nijar.

Sumamen na zuwa ne bayan da shuwagabannin kungiyar kasashen ECOWAS suka tattauna akan batun hare-haren da yan kungiyar ta boko haram suke kaiwa a kasar Najeriya, iyakar kasar Chadi, Kamaru da kasar Nijar.

Aikin ya gudana a wani tsibirin Lake Chad da kogin Komadougou Yobe wanda yake iyaka tsakanin Nijar da Najeriya wanda ya sha fama da hare-haren mayakan kungiyar ta boko haram.

Rundunar sojin kasar ta Nijar tace bata rasa jami’i da kayan aiki ko guda daya ba, sai dai ta bayyana ta samu kwace makamai da suka hadar da motoci, bindigogi da makamai masu linzami.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog