Man City ta doke Liverpool 2-1

Karatun minti 1

Liverpool tayi rashin nasara a hannun takwararta ta Manchester city mai rike da kambun gasar firimiyar ta kasar Ingila.

Wasan da aka buga a jiya alhamis ya ja hankalin magoya bayan kwallon kafa a fadin duniya, wasan da akeyiwa kallon mafi zafi a kakar wasannin bana ta firimiyar.

Dan wasan Man city Sergio Ageuro shine ya fara jefa kwallo a minti na 40 , bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma dan wasan Liverpool Roberto Firmino ya farke a minti na 64 inda daga bisani kuma Leroy Sane yaci kwallon data bawa Man city jan ragamar wasan tare da tafiya da maki uku a minti na 72.

Liverpool dai itace mai jan ragamar gasar ta firimiya inda tabawa Man city ratar maki 4.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog