/

Jirgin sojin Najeriya ya fadi a Borno

Karatun minti 1

Jirgin  mai saukar ungugulu mallakar sojin saman Najeriya ya fado yayin da yake mayar da martanin hare-hare da yan tada kayar baya suke kaiwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Har zuwa yanzu babu rahoto na silar faduwar jirgin, ko kuma adadin rauni ko rayuka da aka rasa a lokacin hadarin.

Mai magana da yawun rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola a wata sanarwa daya  fitar ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda yace al’amarin ya faru ne a lokacin da rundunar ke aika hare-hare zuwa ga sansanonin masu tada kayar bayan a kokarinsu na ganin su kawar da mayakan kungiyar ta boko haram wanda suka addabi arewa maso gabashin kasar ta Najeriya.

Tun kafin shigowar sabuwar shekara a baya-baya, kungiyar ta boko-haram suka shiga kai hare-hare masu zafi a jihar Borno.

Masana na ganin hakan babbar barazana ce ga tsaron kasar na lokacin da ya rage kasa da wata daya a gudanar da babban zaben kasar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog