(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Tankar mai ta kone Almajirai 3, matar aure da wasu mutum 8 a yayin ɗiban fetur bayan motar ta faɗi

dakikun karantawa

Rahotanni  sun bayyana yadda wasu al’amajirai guda 3 tare da wasu mutum 8 suka kone kurmus yayin da wata tankar mai ta kama da wuta a unguwar Gawu da ke Abaji a birnin Abuja.

DABO FM ta tattara cewar har kawo yanzu ba a iya bayyana sunayen al’amajiran da al’amarin ya ritsa da su ba.

Daga cikin wadanda suka kone sun hada da shugaban ‘yan sa ka na unguwar, Adamu Ibrahim, Dantala Usman, Umar Aliyu, Muhammad Hamza, Hassan Usman, Gambo Hamisu, Sani Abdulmalik da wata matar aure mai suna Halima Muhammad Yusuf, kamar yadda DailyTrust ta rawaito.

Wani mazaunin yankin, Usman Yakubu ya bayyana yadda al’amarin ya faru. Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:23 na safe bayan da motar man ta yi yunkurin kaucewa haduwa da wata babbar mota ta kamfanin ‘Dangote.’

Ya ce “motar man ta taho ne daga sashin Lapai in da ta nufi Izom, bayan ta kauce wa wani rami a kan titin, motar ta kwace ta yi gefen titi. Man ya fara zubewa daga gefen titin.”

Ya sake bayyana cewar “faduwar motar ke da wuya wasu daga cikin mazauna unguwar su ka taho a guje da bokitansu da jarkoki domin kwasar man da yake zubowa daga motar.”

“A yayin da suke ɗibar man, motar ta kama da wuta tare ta kone almajirai 3 da wasu mutum 8 ciki har da wata matar aure da ta zo korar yara daga wajen.

Mai unguwar Gwaji, Alhaji Yusuf Ibrahim ya tabbatar da faruwar al’amarin, ya ce tuni ma dai aka birne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog