Ƙungiyar Kano Pillars da a ke wa take da ‘Sai Masu Gida’ sun samu nasara a kan takwararsu ta Ifeanyi Ubah a yau Litinin a gasar Firimiya League ta Najeriya.
An tashi wasan in da Pillars ta jefa ƙwallo ɗaya mai ban haushi a ragar Ifeanyi Ubah.
Wasan da aka buga a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke birnin Fatakwal ya sa Pillars ta ɗare kan matsayi na 3 a kan teburin gasar.
DABO FM ta tattara cewar ɗan wasan ƙungiyar Pillars, Auwalu Ali Mallam ne ya jefa wa ƙungiyar ƙwallon a minti na 23. Ƙwallon ita ce ƙwallo ta da ɗan wasan ya ci a kakar bana.
Mutum 10,000 ne suka samu halartar wasan.